Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wuta abar kewayewace da al'amuran da rai take son sha'awrsu na aikata abubuwan da aka haramta, ko takaitawa a wajibai; Duk wanda ya bi son ransa a hakan to ya cancanci wuta, Kuma cewa Aljanna abar kewayewace da al'amuran da rai take kin su; kamar lazimta akan abubuwan da aka umarta da barin abubuwan da aka haramta, da hakuri akan hakan, idan ya kutsa kuma ya yaki ransa a hakan to ya cancanci shiga Aljanna.