Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa aljanna da wuta suna kusa da mutum kamar kusancin igiyar takalmin da yake kasancewa akan bayan kafa, domin kuwa mutum zai iya aikata wani aikin biyayya na yardar Allah - Mai girma da daukaka - da zai shiga aljanna da shi, ko sabon da zai zama sababi na shiga wuta.