Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin hani daga wofintar da gidaje daga sallah sai su zama kamar makabartu, da ba'a sallah a cikin su. Kuma ya yi hani daga maimaita ziyarar wani kabari da taruwa a wurinsa ta fuskar al'ada; domin hakan hanya ce zuwa ga shirka, Ya yi umarni da yin salati da sallama a gare shi a kowane wuri anan doron kasa; domin cewa hakan yana isa gare shi daga na kusa da na nesa duk daya ne, babu bukatuwa zuwa kaikawo a kabarinsa.