Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a cikin masallacinsa a tare da shi akwai sahabbansa, sai wani balaraben ƙauye ya zo daga ƙauye, sai ya zauna yana yin fitsari a grfen masallaci. Sai sahabbai suka yi masa tsawa suka ce: Tsaya tsaya. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ku ƙyale shi, kada ku yanke masa fitsarinsa, sai suka barshi har sai da ya gama. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kirashi sai ya ce masa: Lallai masallatai badan fitsari aka yi su ba, ko nau'ikan ƙazanta ba, kawai su dan ambatan Allah ne - Mai girma da ɗaukaka -, da sallah, da kuma karatun alƙur'ani da makamancin haka. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya umarci wani mutum daga cikin sahabbai sai ya zo da guga cike da ruwa sai ya zuba akan fitsarinsa a hankali.