Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiryar da al'ummarsa addu'ar da ake faɗa a yayin shiga masallaci: (Ya Allah ka buɗe min ƙofofin rahamarKa), sai ya roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sawwaka masa hanyoyin rahamarSa, idan ya yi nufin fita, to, ya ce: (Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa), sai ya roƙi Allah daga falalarSa da ƙarin kyautatawarSa daga arziki na halal.