Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana umartar masu yin sallah kan su daidaita sahunsu, kuma kada sashinsu ya gabata akan sashi kada kuma ya jinkirta, kuma daidaita sahu yana daga cikar sallah , kuma karkace sahu ɓaci ne da tawaya a sallah.