explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum ya yi sallah shi kaɗai a bayan sawu, sai ya umarce shi ya sake sallarsa; domin sallarsa ba ta inganta ba a wannan halin.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kwaɗaitarwa akan gaggawar zuwa sallar jam’i da halartarta, kuma kada ya yi sallah a bayan sawu shi kaɗai dan kada ya bijirar da sallarsa ga ɓaci.
  • Ibnu Hajar ya ce: Wanda ya fara sallah shi kaɗai a bayan sawu sannan ya shiga cikin sawu kafin ɗagowa daga ruku'u to sakewa ba ta wajaba gare shi ba, kamar yadda yake a cikin hadisin Abu Bakrata, inba haka ba to yana wajaba abisa gamewar hadisin Wabisah.