Bara'au Dan Azib - Allah Ya yarda da shi - yana bada labari alhali shi mai gaskiyane, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya ɗago kansa daga ruku'u kuma ya ce: Sami'al lahu liman hamidahu (Allah Yaji wanda ya gode maSa), wanda ke bayansa ba ya gushewa a tsaye, kuma wani ba ya sunkuyar da bayansa dan yin sujjada har sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanya goshinsa akan ƙasa, sannan su faɗi suna masu sujjada a bayansa.