Daga Abdullahi Bn Abbas -Allah ya yarda da su- ya ce: "Na iso akan Jaka, kuma ni a lokacin na kusa Balaga, kuma Manzon Allah SAW yana Sallah da Mutane a Minna ba yana kallon Garu ba, na wuce ta gaban Sahu, sai na sauka, sai na saki Jakar tana kiwo, na shiga Sahu, babu wanda yai mun Inkarin hakan"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi