Annabi ya shiryar da mamu izuwa Hikimar da ta sa aka sanya Limami kuma ita ce cewa duk wanda ya bishi Sallah to yayi koyi da shi a Sallarsa, kuma kada ya saba Masa da wani aiki na ayyukan Sallah, kuma ya kula da duk motsinsa a tsare to idan yai kabbarar harama, to kuyi harama kuma, kuma idan yayi ruku'u to kuyi ruku'i bayansa, kuma idan ya tunasar da ku cewa Allah yana amsa fadin wanda ya gode masa to ku godewa Allah da fadinku, kuma wata sigar ta zo daban kamar ya Ubangiji Ubangijinmu godiya a gareka, kuma idan yayi sujada to ku bishi kuma kuyi sujad, kuma idan yai sallah a zaune -sabida gajiyawa ga barin iya tsayiw- to sabida tabbatar da biyayya kuma kuyi sallah a zaune kuma koda zaku iya tsayiwa.