Annabi -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya tabbatar da cewa idan dai ba'a daidaita sahun Sallah ba to zai sassaba fuskokin wadan da sahun su ya karkace basu kuma daidaita shi ba, cewa lallai lokacin da wasu zasu wuce gaban wasu a sahu, kuma su bar kofofi a tsakaninsu, kuma Annabi -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana koyar da sahabbansa da magana kuma ya shiryar da su da aiki, don ya tsaya yana daidaita su da Hannunsa, hai sai da Annabi ya tabbatar sun fahimci shi kuma sun koya, a cikin wata Sallah daga cikin Salloli sai yaga wani daga cikin Sahabbansa ya turo cikinsa a sahu a tsakanin Abokan Sallar sa sai Annabi yayi fushi kuma ya ce : " kodai ku daidaita Sahunku ko kuma Allah ya sassaba tsakanin fuskokinku".