Daya daga cikin sahabbai mata ta kawo koken zubar jini (jinin Istihara) zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da take fama da shi, sai ya umarceta ta dakatar da sallah gwargwadan abinda hailarta take tsareta kafin zuubar wannan al'amarin da ya faru da ita, sannan ta yi wanka ta yi sallah, ta kasance tana wanka dan neman lada a kowacce sallah.