Annabi -tsira da amincin Allah ya umarci Ummu Habiba da ta yi wanka, a lokacin da ta tambayi shi abin da za ta yi game da jinin istihadha da take fama da shi, don ta kasance tana yin wanka a kowace salla, kuma ta yi fama da jinin istihadwa tsawon shekara bakwai.