Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi girman mutane a kyauta, ya kasance kyautarsa tana yawaita a cikin watan Ramadan lokacin da ya kasance yana bada abinda yake kamata ga wanda ya kamata, kuma sababi a cikin ƙaruwar kyautarsa abubuwane biyu: Na farko: Haɗuwarsa da Jibril - aminci ya tabbata agare shi -. Al'amari na ƙarshe: Karatun AlƘur'ani, shine karatu na zuciya. Sai nazarin da Jibril - aminci ya tabbata agare shi - yake yi da shi dukkan abinda ya sauka na AlƘur'ani ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne mafi kyauta mafi yawan bayarwa kuma mafi aikata alheri, kuma mafi gaggawar anfanar da halitta daga iska mai daɗi wacce Allah Yake aikota da girgije da kuma rahama.