Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa akwai nauyi akan kowanne musulmi a cikin zamantakewa da zai kula da ita kuma take akan sa, Shugaba da sarki mai kiwo ne a abinda Allah Ya ba shi kulawarsa, to ya wajaba akansa kiyaye shari'unsu, da kiyayesu daga wanda zai zalincesu, da yakar makiyinsu, da rashin tozarta hakkokinsu, Mutum a iyalan gidansa wanda aka dorawa tsayuwa kula da su ne da ciyar da su, da kyakkyawar mu'amala, da koyar da su da ladabtar da su, mace a cikin gidan mijinta mai kiwo ce ta hanyar kyawun sarrafa gidansa, da tarbiyyar 'ya'yansa, kuma ita abar tambaya ce game da hakan, bawa wanda aka mallaka da wanda aka yake aiki a biya shi abin tambaya ne a dukiyar mai gidansa ta hanyar tsayuwa da kiyaye abinda ke hannunsa daga gare shi , da hidimarsa, kuma shi abin tambaya ne game da hakan, kowanne mutum mai kiwo ne a abinda aka ba shi kiwon sa, kuma kowa abin tambaya ne game da abin kiwonsa.