Abu Katadah alAnsari - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana binciken wani wanda yake binsa bashi wanda yake ɓoye masa, sai ya same shi, sai wanda ake bi bashi ya ce: Lallai ni bani da kuɗi, kuma bani da dukiyar da zan biya bashinka. Sai Abu Katadah - Allah Ya yarda da shi - ya sa ya rantse da Allah cewa shi bashi da dukiya? Sai ya rantse da Allah cewa shi mai gaskiya a abinda yake faɗa. Sai Abu Katadah - Allah Ya yarda da shi - ya ce lallai shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Wanda yake so kuma yake farin ciki Allah Ya tseratar da shi daga baƙin cikin ranar alƙiyama da tsanace-tsanancanta da tsorace-tsoracenta, to ya yayewa wanda yake cikin ƙunci, shi ne cewa ya ƙara (lokaci) ya jinkirta neman bashin, ko ya sarayar da sashin bashin ko ma dukkansa.