Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari, Cewa cikakken mutum a sada zumunci da kuma kyautatawa 'yan uwa shi ne mutumin da yake fuskantar kyakkyawa da kyakkywa, Kai mai sadarwa a hakika a sada zumunci shi ne wanda idan an yanke zumuncinsa sai ya sadar da shi, idan sun munana masa to sai shi ya fuskantarsu da kyautatawa zuwa garesu.