Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah Yana son ɗabi'u uku daga bayinSa, kuma Yana ƙin abubuwa uku daga gare su, Yana so daga garesu: Su kaɗaita Shi da bauta kada su taranya wani abu a cikin bautarSa, kuma su yi riƙo da alƙawarin Allah da kuma Alƙur'ani da sunnar AnnabinSa bakiɗaya, kada su rarraba daga jama'ar musulmai. Kuma yana ƙi musu: zance mara anfani da yasasshiyar magana a cikin abinda babu ruwansu, da kuma tambayar abinda bai afku ba, ko roƙon mutane dukiyoyinsu, da kuma abinda ke hannunsu, da kuma abinda ba'a buƙatarsa, da tozarta dukiya da bada ita ba ta fuskar shari'a ba, da kuma bijiro da ita ga abinda zai lalata ta.