Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ka taimaki ɗan'uwanka azzalimi ko wanda aka zalinta». Sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, zan taimake shi idan ya kasance wanda aka zalinta ne, shin kana ganin idan ya zama azzalimi ta yaya zan taimake shi? ya ce: «Ka kare shi - ko ka hana shi - daga zalinci; domin cewa hakan taimakonsa ne». Ingantacce ne - Bukhari ne ya rawaito shi
explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci musulmi da ya taimaki ɗan'uwansa musulmi, daidai ne ya kasance azzalimi ne ko wanda aka zalinta, sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, zan taimake shi idan ya kasance wanda aka zalinta ne, shi ne in hana a zalince shi, shin kana ganin idan ya zama azzalimi ta yaya zan taimake shi? Ya ce: Ka hana shi ka yi riƙo da hannunsa ka kare shi, ka hana shi zalincin; domin hakan shi ne taimakonsa akan Shaiɗaninsa da kuma ransa mai umartarsa da mummunan aiki.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Faɗakarwa akan wani haƙƙi daga cikin haƙƙoƙin 'yan uwantaka ta imani tsakanin musulmai.
  • Riƙo da hannun azzalimi, da kuma hana shi zalinci.
  • Yadda Musulunci ya saɓawa fahimce-fahimcen Jahiliyya, inda suka kasance suna taimakekeniya, duk ɗayane sun kasance waɗanda aka zalinta ne ko masu zalintar wasunsu ne.