Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin bana baku labarin abin da ya fi ladan nafilar azimi da sallah da sadaka ba? Suka ce: Eh.. Ya ce: Yin sulhu tsakaknin masu rigima inda rigima take gadar da rabuwa da kuma kadaita da ƙiyayya da juyawa juna baya tsakanin mutane, domin abin da yake haifuwa akan ɓata waɗanda ke rigima na ƙiyayya wacce ita ce ɗabi'ar da sha'aninta shine ta halakar ta tunɓuke Addini da duniya kamar yadda aska take tunɓuke gashi.