Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Ya wajabta wasu abubuwa kuma Ya faralanta wasu farillai, to ku lazimcesu kada ku yi sakaci a cikinsu ta hanyar barinsu ko wulaƙantar da su, kuma Ya sanya muku shamaki da abubuwan da ya tsawatar abubuwan ƙaddarawa waɗanda zasu kareku kuma su tsawatar da ku daga abin da bai yarda da shi ba, dan haka kada ku yi ƙari kan a bin da shari'a ta yi muku umarni da shi, kuma Ya haramta wasu abubuwan da Ya haramta dan haka kada ku aikata su kai karma ku kusancesu, kuma bayan wannan Ya barsu kuma Ya yi shiru game da su dan rahama ga bayinSa, sai suka wanzu akan asalin halaccinsu dan haka kada ku yi bincike game da su.