Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya aikata wani saɓon da yake wajabta haddin shari'a, kamar zina da sata, sai ya samu uƙubarsa kuma aka tsayar masa da haddi a duniya, to lallai hakan zai shafe masa wannan saɓon, kuma zai shafe uƙubarsa ta lahira; domin cewa Allah Shi ne Mafi karamci kuma Mafi jin ƙan ya haɗawa bawanSa uƙuba biyu. Wanda kuma Allah Ya suturta shi a duniya, ba a yi masa uƙuba ba akan wannan saɓon, kuma Allah Ya yi masa afuwa Ya gafarta masa, to Allah Shi ne Mafi buwaya kuma Mafi girma Mafi karamcin ya dawo da uƙubar zunubin da Ya riga Ya gafarta shi kuma Ya yi afuwarsa.