Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wannan addinin zai game dukkan sasannin ƙasa, duk gurin da dare da rana suka kai gurin to wannan addinin sai ya kai wurin, Allah ba Zai bar wani gida a cikin birni ko alƙaryu ko a cikin ƙauyuka da sahara ba sai Ya shigar da wannan addini cikinsa. Wanda ya karɓi wannan addinin kuma ya yi imani da shi to zai zama mabuwayi da buwayar musulunci, wanda ya bijire masa kuma ya kafirce masa to zai zama ƙasƙantacce wulaƙantacce. Sannan sahabi Tamimud Dari - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa shi ya ga abinda manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata gare shi - ya bada labari da shi a iyalan gidansa musamman, domin wanda ya musulunta daga cikinsu alheri da ɗaukaka da buwaya sun same shi, wanda kuma ya kafirce daga cikinsu ƙasƙanci da wulaƙanci sun same shi tare da abinda zai dinga bayarwa na dukiya ga musulmai.