Daga Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shigo wurina, hakika na rufe jarkata da wani labule a jikinsa akwai hotuna, lokacin da ya gan shi sai ya yaye shi, fuskarsa ta janza ya ce : "Ya A'isha, Mafi tsananin azaba a wurin Allah a ranar Alkiyama wadanda suke kwaikwayon halittar Allah" A'isha ta ce: "Sai muka yanke shi sai muka maida shi shinfida ko shinfidu biyu". Ingantacce ne - Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga dakinsa ga A'isha - Allah Ya yarda da ita - sai ya sameta ta rufe jarkarta karama wacce take sanya kayanta a ciki da wani yanki a jikinsa akwai hotunan masu rayuka, sai launin fuskarsa ya canja dan fushi saboda Allah sai ya cire shi, ya ce: Mafi tsananin azaba a ranar Alkiyama wadanda suke kamanta halittar Allah da hotunansu. A'isha ta ce: sai muka maida shi shinfida ko shinfidu biyu.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Hana abin ki a lokacin ganinsa da rashin jinkiri a hakan, muddin dai babu wata barna mafi girma a hakan.
  • Azabar ranar Alkiyama tana banbanta a tsanani gwargwadan girman zunubi.
  • Yin hoton abubuwa masu rai yana daga manyan zanubai.
  • Yana daga hikimomin haramta hoto kamanceceniya da halittar Allah - Madaukakin sarki -, duk daya ne mai hoton ya yi nufin kamanceceniya ne ko bai yi nufi ba.
  • Kwadayin shari'a akan kiyaye dukiyoyi ta hanyar fa'idantuwa daga gare su bayan an nisantarsu abinda ya haramta a cikinsu.
  • Hani akan kera zanen abubuwa masu rai akan kowanne yanayi ya kasance, koda sun kasance a wulakance ne.