Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin sashin siffofin 'yan aljanna da 'yan wuta. Mafi yawancin 'yan aljanna sune: "Dukkan mai rauni mai ƙanƙar da kai", wato: Mai ƙanƙan da kai mai ƙanƙanr da kai ga Allah - Maɗaukakin sarki -, mai ƙasƙantar da kansa gareShi, har takai wasu daga mutane suna raunana shi kuma suna wulaƙanta shi, wannan mai ƙasƙantar da kai ga Allah - Maɗaukakin sarki - da zai yi rantsuwa da Allah dan kwaɗayi a cikin karamcin Allah - Maɗaukakin sarki -, da Allah Ya kuɓutar da shi, kuma Ya tabbatar masa da abinda ya yi rantsuwa akansa kuma Ya amsa buƙatarsa da addu'arsa. Kuma mafi yawancin 'yan wuta su ne: Dukkan "Mai ƙaton ciki" shi ne mai kaushin zuciya, mai bushewar zuciya mai tsananin husuma, ko mai alfasha wanda ba ya jawuwa ga alheri, "Mai yawan girman kai" shi ne mai girman kai, mai yawan ci, mai ƙiba, mai taƙama a tafiyarsa, mai mummunar ɗabi'a, "Mai girman kai" saboda butulcewarsa ga gaskiya, da kuma wulaƙanta waninsa.