Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ba wa sahabbansa labari game da Dajjal da siffofinsa da almominsa da abinda wani annabi a gabaninsa bai zantar da shi ba, daga hakan: Cewa shi mai ido ɗaya ne. Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanya masa kwatankwacin aljanna da wuta, gwargwdan ganin ido. Sai dai aljannarsa wuta ce, kuma wutarsa aljanna ce, wanda ya bi shi zai shigar da shi wannan aljannar a abinda mutane suke gani, sai dai cewa ita wuta ce mai ƙuna, wanda ya saɓa masa zai shigar da shi wutar a abinda mutane suke ganinsa, sai dai ita aljanna ce mai daɗi. Sannan annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga fitinarsa kamar yadda (Annabi) Nuhu ya gargaɗar da mutanensa shi.