explain-icon

Bayani

Nana A'isha uwar Muminai Allah Ya yarda da ita, tana ba da bayanin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana tsananin kwaɗayi a kan yin ambaton Allah maɗaukaki, kuma ya kasance yana ambaton Allah a kowanne lokaci da kowanne yanayi.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Ba a sharɗanta tsarkin ƙaramin hadasi ko babba a ambaton Allah ba.
  • Dawwamar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a ambaton Allah maɗaukaki.
  • Kwaɗaitarwa a kan yawaita ambaton Allah maɗaukaki a kowanne lokaci domin koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai a yanayin da aka hana ambaton Allah kamar lokacin biyan buƙata.