explain-icon

Bayani

Abu Sa'idul Khudr - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi tsananin kunya daga yarinya budurwa wacce bata yi aure ba, ba ta yi mu'amala da maza ba wacce ke suturce a cikin gidanta, yana daga tsananin kunyarsa cewa shi idan ya ki wani abu fuskarsa tana canjawa kuma ba ya magana, kai sahabbansa suna fahimtar kinsa ga hakan a fuskarsa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Bayanin abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kunsa akansa na kunya, ita ce ɗabi'u masu girma.
  • Kunyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - muddin dai ba'a keta alfarmomin Allah, idan an keta su; to shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana fushi yana umartar sahabbansa kuma yana hanasu.
  • Kwaɗaitarwa akan ɗabi'antuwa da kunya; domin ita tana sawa rai aiki mai kyau da barin mummuna.
explain-icon

Kari