Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa wani mutum daga cikin mutanen Madina yana daga cikin mafi nisan gida daga masallacin Annabi, kuma ya kasance sallah bata wuce shi; kai yana halattar kowace sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai aka ce masa: Inama dai a ce zaka sayi jakin da zaka dinga hawansa a cikin duhun dare da kuma cikin zafin ƙasa a cikin rana, ya ce: Bana son a ce gidana yana gefen masallaci, lallai ni ina son Allah Ya rubuta mini tafiyata zuwa masallaci, da kuma dawowata idan na dawo zuwa ga iyalaina, sai maganarsa ta kai wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: «Haƙiƙa Allah Ya haɗa maka hakan baki ɗayansu».