Wani mutum ya zo gurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: dan ya tambaye shi ya nemi fatawarsa game da hukuncin mutumin da yake fita yaƙi yana neman lada daga Allah da kuma kwaɗayin yabo da godiyar mutane, shin zai samu lada? sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bashi amsa: Da cewa bashi da komai na lada; dan abinda ya yi wa Allah tarayya da shi a cikin niyyarsa, sai mutumin ya maimaita tambayarsa sau uku ga Annabi - tsira da amincin Allaah su tabbata agare shi -, kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana amsa masa wannan amsar; da cewa bashi da lada, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bashi labarin cewa ka'idar karbar aiki a wurin Allah: Lallai cewa Allah ba Ya karbar aiki sai in ya zama dukkansa saboda Allah ne batare da tarayya da wani a cikinsa ba, kuma ya zama dan zatin Allah ne - tsarki ya tabbatar maSa -.