Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari: Game da mutumin da ya kasance yana mu'amalar bashi tare da mutane, ko ya siyar bashi, Ya kasance yana cewa yaronsa wanda yake karbo masa basukan dake hannun mutane: Idan ka je wurin wanda ake bi bashi kuma ba shi da abinda zai biya bashin dake kansa dan gajiyawarsa "To ka kau da kai gare shi"; ko dai da jinkirta masa da rashin nace masa a kan ya biya., Ko da karbar abinda ke tare da shi koda tare da abinda ke cikinsa ne na tawaya, hakan dan kwadayi daga gare shi akan Allah Ya ketare masa kuma ya yi masa rangwame. Lokacin da ya mutu sai Allah ya yi masa afuwa kuma ya ketare daga munanan ayyukansa.