explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya ci ko ya sha akan mantuwa alhali shi yana cikin azimin farilla ko nafila to ya cika aziminsa kada ya karya; domin cewa shi bai yi nufin karyawa ba, kawai shi wani arziƙi ne Allah Ya koro masa kuma Ya ciyar da shi Ya shayar da shi.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Ingancin azimin wanda ya ci ko ya sha akan mantuwa.
  • Babu zunubi akan wanda ya ci ko ya sha akan mantuwa; domin cewa shi bada zaɓinsa ba ne.
  • Sauƙin Allah ga bayinSa da sauƙaƙa musu da ɗauke wahala da ƙunci daga gare su.
  • Mai azimi ba ya karya aziminsa da wani abu daga abubuwa masu karya azimi sai idan sharuɗɗa uku sun cika: Na farko: Ya zama masani, idan ya kasance jahili bai karya azimi ba. Na biyu: Ya zama yana mai tinawa, idan ya kasance yana mai mantuwa, to aziminsa ingantacce ne kuma babu ramuwa akansa. Na uku: Ya zama yana mai zaɓi ba abin tilastawa ba shi ne ya ci abinda yake karya azimi da zaɓinsa.
explain-icon

Kari