Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta yi bayanin sallar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana buɗe sallarsa da kabbarara harama, sai ya ce: «Allahu Akbar (Allah ne Mafi girma)», kuma yana buɗe karatu da Suratul Fatiha: «Alhamdu lillahi rabbil aalamin (Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai)...». Ya kasance idan ya yi ruku'u bayan tsayuwa, ba ya ɗaga kansa sama kuma ba ya sunkuyar da shi a lokacin ruku'u, kawai yana maida shi daidai wa daida, idan ya ɗago kansa daga ruku'u sai ya tsayu a tsaye kafin ya yi sujjada, idan ya ɗaga kansa daga sujjada ta farko, ba ya sujjada ta biyu har sai ya tabbata a tsaye. Ya kasance yana zama bayan kowanne raka'o’i biyu dan yin tahiya kuma yana cewa: «Attahiyyatu lillahi was salawat waɗɗaibat(Gaishe-gaishe sun tabbata ga Allah da salloli da tsarkakan ayyuka)...», kuma ya kasance idan ya zauna tsakanin sujjadu biyu ko dan tahiya sai ya shimfiɗa ƙafarsa ta hagu ya zauna a kanta, ya kuma kafa ƙafarsa ta dama. Kuma yana hana mai sallah a cikin sallarsa ya zauna kamar zaman shaiɗan, hakan shi ne ya shimfiɗa ƙafafuwansa akan ƙasa, kuma ya zauna akan ƙarshensu, ko ya ɗanfara mazaunansa a ƙasa ya kafa ƙwaurukansa ya kuma ɗora hannayensa akan ƙasa kamar yadda kare yake yi, ko mai sallah ya shimfiɗa zira'insa ya shimfiɗasu a cikin sujjada kamar yadda namun daji suke yi . Kuma ya kasance yana cika sallarsa da yin sallama: «Assalamu alaikun warahmatullah» daga dama sau ɗaya, ɗayan kuma daga hagu.