Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga yin rantsuwa tare da sanin mai rantsuwar cewa shi maƙaryaci ne a cikinta, dan ya ya karbi dukiyar waninsa; to zai gamu da Allah alhali Yana mai fushi da shi. Sai Ash'As ɗan Ƙais - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa , Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi hakan lokacin da ya kasance akwai rigima ta mallakar wani fili tsakaninsa da wani mutum cikin Yahudawa, sai suka kai ƙara zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya cewa Ash'As: Wajibi ne ka zo da shaidun da suke tabbatar da abinda kake ƙararsa, idan ka kasa to baka da wani abu sai rantsuwar abokin rigimarka wanda ake ƙararsa, sai al-Ash'As ya ce: Ya manzon Allah, to bayahude zai rantse kuma ba ya taka tsantsan ya tafi da dukiya ta, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da gasgata hakan a cikin Alƙur'ani a faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -: {Lallai waɗanda suke musanya}. Suke canja {da alƙawarin Allah}, da wasiyyarSa ga muminai da dawo da amana {da rantse-rantsensu} da rantsuwarsu da sunanSa suna maƙaryata {ɗan kudi kaɗan} na rabon duniya {To waɗannan basu da wani rabo a lahira} kuma basu da wani nasibi {Kuma Allah ba Zai yi musu magana ba}, da zancen da zai faranta musu rai ya amfanar da su ba, kai ya yi fushi da su, {Kuma ba Zai kallesu ba a ranar alƙiyama} kallo na rahama da kyautatawa, {Kuma ba Zai tsarkakesu ba} da yabo mai kyau ba, kuma ba Zai tsarkakesu da gafara daga zunubai da datti ba {Kuma azaba mai raɗaɗi ta tabbata a garesu} mai sa ciwo saboda abinda suka aikata.