Hindu 'yar Utbah - Allah Ya yarda da ita - ta nemi fatawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mijinta Abu Sufyan - Allah Ya yarda da shi -, kuma shi mutum ne marowaci mai kwaɗayin dukiyarsa, ba ya bata abinda zai isheta ya ishi 'ya'yanta na ciyarwa, sai dai in ta ɗauka a ɓoye cikin dukiyarsa alhali shi bai sani ba, shin akwai wani laifi akanta a hakan? Sai (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ki ɗauki gwargwadan abinda aka sani a al'ada cewa shi zai isa cikin dukiyarsa koda ba tare da saninsa ba.