explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa sadaka ba ta rage dukiya, kai! tana tunkuɗe masa illoli, kuma Allah Yana musanyawa mai ita da alheri mai girma, sai ta zama ƙari ba ragi ba. Kuma afuwa tare da iko a kan ramuwa ko kama (mai laifin), ba sa karawa mai yinsu komai sai ƙarfi da buwaya. Kuma wani ba zai ƙanƙan da kai, ya ƙasƙanta ga Allah ba, ba don tsoron wani ba, ba don yaudara (na nuna tausayi) gareshi ba, ba don neman wani abin amfani daga wajensa ba, sai sakamkonsa ya zama ɗaukaka ne da sharafi.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Alheri da rabauta (suna ) cikin kamanta shari'a da aikata alheri ko da wasu daga mutane sun yi zaton cewa saɓanin hakan ne.