explain-icon

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana zama a kan kaburbura. Kamar yadda ya hana yin Sallah ana kallon kaburbura, ta yadda kabari zai kasance ta inda alƙiblar mai Sallah take, domin hakan hanya ce ta shirka.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Hana yin sallah a maƙabartu, ko tsakanin kaburbura, ko ana kallon kaburbura, sai dai Sallar janaza kamar yadda hakan ya tabbata a Sunnah.
  • Hana yin Sallah ana kallon kaburbura don toshe ƙofar kaiwa ga shirka.
  • Musulunci ya hana wuce iyaka a kan kaburbura ya kuma hana wulaƙantasu, ba wuce iyaka, kuma ba wulaƙantawa.
  • Alfarmar Musulmi tana nan bayan rasuwarsa, saboda faɗin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: Karya ƙashin mamaci kamar karya shi yana raye ne.