Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mutum ba ya zama mumini mai cikakken imani na wajibi har sai soyayyarsa ta zama mai bi ga abin da Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo da shi na umarni da hani da wasunsu, sai ya so abin da ya yi umarni da shi, ya kuma ƙi abin da ya yi hani daga gare shi .