Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa shi ya kasance yana cikin shayar da wanda yake cikin gidan mijin babarsa Abu Ɗalha - Allah Ya yarda da shi -, giyarsu ta kasance a wannan lokacin ita ce tsimi, shi ne cakuɗa bushasshen dabino da 'ya'yansa kafin ya zama ɗanye, sai ga mai kira daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kira: Ku saurara lallai cewa giya haƙiƙa an haramtata, ya ce: Sai Abu Ɗalha ya ce da ni: Ka fita, ka zubar da ita, sai na fita sai na zubar da ita, sai giyar ta kwarara a lungunan Madina, sai wasu daga mutane suka ce: Haƙiƙa an kashe (a jihadi) wasu sahabbai kafin haramtata alhali ita tana cikin cikinsu, sai Allah Ya saukar da: {Babu laifi akan waɗanda suka yi imani kuma suka aikata aiki na gari a abinda suka dandana} [al-Ma'ida: 93] Aya. Wato: Babu zunubi akan waɗanda suka yi imani a cikin abinda suka dandana kuma suka sha na giya kafin haramtata.