Abdullahi ɗan mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ambata a cikin faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Duk wanda ya nufe shi da wata fanɗara da zalinci to zamu ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi}. [al-Hajj: 25], ya ce: Da ace wani daga cikin mutane zuciyarsa zata zantar masa cewa ya yi nufin aikata wani mummunan aiki a cikin Haramin Makka wanda zai halatta abinda Allah Ya haramta masa a cikinsa na haram da harshe ne ko kisa da gangan to cewa hakan zalinci ne, kuma da a ce ƙudirin niyyar a birnin Adan ne a cikin (kasar) Yaman to lallai shi mai cancantar Allah Ya azabtar da shi ne da azaba mai raɗaɗi saboda hakan, koda kuwa bai aikata shi ba, niyyar hakan kawai ta ishe shi .