Nu'umanu Ibnu Bashir - Allah Ya yarda da su - ya ambaci cewa shi yana zaune a wajen mimbarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ji wani mutum yana cewa: Bayan na musulunta ba zan damu dana aikata wani aiki ba sai dai in shayar da mai aikin Hajji. Wani kuma ya ce: Bayan na musulunta ba zan damu dana aikata wani aiki ba sai dai in raya Masallaci mai alfarma. Wani kuma ya ce: Jihadi a tafarkin Allah ya fi abin da kuka faɗa. Sai Umar Ibnul Khaɗɗabi - Allah Ya yarda da shi- ya yi musu tsawa saboda ɗaga muryarsu da suka yi a wajen mimbarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma safiyar ranar Juma'a ce, sai dai idan na yi sallar Juma'a zan shiga in tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kan abin da kuka saɓa a cikinsa, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Shin, kun mayar da shãyar da mahajjata da rãyar da Masallaci Mai alfarma kamar wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya yi jihãɗi a cikin hanyar Allah? Bã su daidaita a wurin Allah. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai} [al-Tauba: 19].