Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aiki wata runduna, sai ya sanya wani mutum daga cikin mutanen Madina shugaba a kansu, kuma ya umarcesu da su yi masa biyayya, sai shugaban ya yi fushi a kansu kuma ya ce musu: Shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai umarceku ku bini ba? Suka ce: Ya yi umarni, ya ce: To na umarceku ku tattara mini itace ku kunna wuta, sannan ku shiga cikinta, sai suka tara itatuwa suka kunna wuta, lokacin da suka yi yunkurin shiga cikinta, sai sashinsu ya fara kallon sashi. Suka ce: Lallai mu bamu bi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba sai donin gujewa wuta shin ma shigeta kuwa? Suna cikin haka sai wutar ta mutu, kuma fushin shugaba ya tafi. Sai aka baiwa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - labarin hakan, sai ya ce: Da sun bi shi sun shiga cikin wutar da suka kunnata da an yi musu azaba a cikinta har ƙarewar duniya, babu biyayya ga wani abin halitta a cikin saɓon Mahalicci; kaɗai biyayya tana wajaba ne a aikin alheri ba'a saɓo ba.