Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana faɗa a cikin Hadisi Ƙudsi: Mutumin da yake zagin zamani a lokacin saukar masifu da abubuwan ƙi yana cuta ta kuma yana tauyeNi; domin cewa Shi - tsarki ya tabbatar maSa - Shi ne Mai jujjuya al'amura Shi kaɗai, kuma Mai sarrafa abinda yake faruwa; to aibata zamani aibata Allah ne - Mai girma da ɗaukaka -, zamani kuwa kawai shi halitta ne abin horewa, abubuwa suna gudana ne a cikinsa da umarnin Allah - Maɗaukakin sarki -.