explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana son addu'o'i masu tattaro alherin duniya da lahira wacce lafazinta kaɗan ne kuma ma'anarta yana da yawa, kuma a cikinta akwai yabo ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da manufofi na gari, kuma yana barin koma bayan haka.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • An so addu'a da lafuza sassauƙa masu tattaro ma'anonin alheri, da kuma ƙin ɗorawa kai wahala da tsananatawa a cikin mas'ala, hakan saɓanin karantarwar Annabi ce - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • An keɓanci Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kalmomi masu tattaro (ma'anoni).
  • Kwaɗayi akan abinda ya tabbata cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da shi; koda ya kasance mai tsawo ne, kuma kalmominsa sun yi yawa, dukkansa daga addu'o'i ne masu tattarowa.