Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana gargaɗI akan nau'i biyu daga mutane cikin 'yan wuta bai gan su ba, kuma ba'a samesu a zamaninsa ba, kawai za su kasance ne a bayansa: Nau'i na farko: Wasu mutane ne a tare dasu akwai bulalai kamar jelunan (bidin) shanu masu tsawo, suna dukan mutane da su, sune 'yan sanda da mataimakan azzalumai waɗanda suke dukan mutane ba tare da wani haƙƙi ba. Nau'i na biyu: Wasu mata ne da suka cire tufafin kamewa da kunya wanda aka ɗabi'anci mace akansa a al'adan ce. Shi Siffantasu da: Masu sanye da tufafi a haƙiƙa, matsiraita a ma'ana; Domin cewa su suna sanye da taufafi shara-shara yana nuna fatar jiki, kuma suna suturce wani abu daga jikinsu suna yaye sashinsa; dan bayyanar da kyaawunsu. masu karkato da zuciyar maza zuwa garesu , saboda tufafin da suka saka, da taƙamarsu a tafiya, masu karkatar da kafaɗunsu, kuma suna karkato da wasunsu zuwa karkacan tunani da bata wanda suka afkawa a cikinsa, Daga siffofinsu: Kawunansu tamkar tozon karkataccen raƙumi ne, suna kuma kara girman kawunan nasu, suna ƙara masa girma ta hanyar rufa masa kari da waninsa, Kamanta su da aka yi da tozon aturkumami kawai dan dago gashinsu ne da faratansu a saman kawunansu, da karairayarsu da abinda zai kitsantar da shi har ya karkace zuwa wani ɓangare daga ɓangarorin kai, kamar yadda tozon raɗumi yake karkacewa. Duk waɗanda suka kasance da waɗan nan siffofin to a tare da su akwai wannan narkon mai tsanani cewa ba za su shiga aljanna ba kuma ba za su ji ƙanshinta ba kuma ba za su yi kusa da ita ba, kuma ƙanshin aljanna ana samunsa ana shaƙarsa daga tafiya mai nisa.