Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga abubuwa huɗu: Na farko: (Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa) ta Addini da duniya kuma in tabbata akan Musulunci, in nisanci faɗawa cikin saɓon da yake gusar da ni'imomi. Na biyu: (Da juyawar lafiyarKa) da canjata zuwa bala'i; to ina roƙonKa dawwamar lafiya, da kuɓuta daga radaɗi da cututtuka. Na uku: (Da shammatar azabarKa) daga bala'i ko saɓo, azaba da uƙuba idan suka zo fuj'a bagtatan, to babu wani lokaci a wannan dan tuba da riska, wanda aka shafa da su zai zama mafi girma kuma mafi tsanani. Na huɗu: (Da dukkan fushinKa) da sabubban da suke wajabta fushinKa; domin wanda Ka yi fushi da shi to haƙiƙa ya taɓe kuma ya yi asara. Haƙiƙa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya zo da lafazin jam'i; dan ya ƙunshi sabubban fushinSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - daga maganganu da ayyuka da ƙudirce-ƙudierce.