Ya kasance daga addu'o'in Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mai tattarowa faɗinsa: "Ya Ubangiji Ka gafarta mini kurakuraina" da zunubina, "da jahilcina' da abinda ya afku daga gareni ba tare da sani ba. "Da wuce gona da iri na a dukkan al'amarina" da kasawata da wuce gona da iri na. "Da abinda Kaine Mafi sani da shi daga gareni" Ka san shi Allah ni kuma na manta shi. "Ya Allah Ka gafarta mini kurakuraina da gangancina" da abinda ya bijiro na ganganci daga gareni da ilimi daga gareni da zunubai. "Da (aiki) da gaske daga gareni da kakaci na" da abinda ya bijiro daga kakaci, da abinda ya afku daga gareni a hali biyun. "Dukkanin wannan daga gareni ne" inda na tattara abinda aka ambata daga zunubai da aibuka. "Ya Allah Ka gafarta mini abinda na gabatar" da abinda ya shuɗe, "da abinda na jinkirtar" a abinda zai zo . "Da abinda na ɓoye" na ɓoye, "da abinda na bayyana" na bayyanar. "Kai ne mai gabatarwa kuma Kaine Mai jinkirtarwa" Kana gabatar da wanda kake so daga halittarKa zuwa rahamarKa da dacewarKa da abinda Ka yarda da shi, kuma Kaine Mai jninkirtarwa Kana jinkirtar da wanda Kake so daga hakan da taɓarwarKa gare shi , bamai gabatar da abinda Ka jinkirtar, kuma ba mai jinkirtar da abinda Ka gabatar daga al'amura. "Kai ne Mai iko akan dukkan komai" Mai cikakken iko Mai cikakken nufi, Mai aikata abinda Ka so.