(Labari) ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana jeranta azimi ba ya ajiyewa tsawon shekara, kuma yana sallar dare gaba ɗayansa ba ya bacci, sai ya hana shi daga hakan, kuma ya ce masa: Ka yi azimi kuma ka huta, ka yi sallar dare kuma ka yi bacci. Kuma ya hane shi daga jeranta azimi da tsayuwar dare gaba ɗayansa, kuma ya ce masa: Lallai cewa kai idan ka aikata hakan idanka zai yi rauni saboda shi zai yi kogo zai shige, kuma zuciyarka zata gaji ta ƙosa saboda haka; babu azimi (ga) wanda ya azimci shekara; inda cewa shi bai samu ladan azimin ba dan saɓawa hani, kuma bai buɗe baki ba domin cewa shi ya kame. Sannan ya shiryar da shi zuwa azimin kwana uku a kowane wata shi ne azimin shekara; domin kowace rana (kwatankwacin ladan) kwanaki goma ne, kuma hakan shi ne mafi ƙarancin riɓanyawa ga kyakkyawa. Sai Abdullahi ya ce: Lallai ni zan iya sama da hakan. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: To sai ka yi azimin (Annabi) Dawud - aminci ya tabbata agare shi - shi ne mafificin azimi, ya kasance yana azimin yini kuma yana hutawa yini, kuma ya kasance ba ya gudu idan ya gamu da maƙiya; domin tsarin aziminsa ba ya raunana jikinsa ba.