Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa masoyinsa kuma abokinsa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa wasicci kuma ya alkawaranta masa ɗabi'u uku: Na farko: Azimin kwana uku a kowane wata. Na biyu: Raka'a biyu ta walaha a kowace rana. Na uku: Witiri kafin bacci; hakan ga wanda ya ji tsoron kada ya farka a ƙarshen dare.