Laƙiɗ Ibnu Sabira - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa shi ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - tare da waninsa daga mutanensa Banul Muntafiƙ, ya ce: Bamu same shi a gidansa ba, sai muka samu Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - sai ta yi umarni a yi mana farfesu na gari da romo, kuma aka kawo mana farantin da a cikinsa akwai dabino. Sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai ya ce: Shin an kawo muku wani abu ne na abinci? Muka ce: Eh, Laƙiɗ ya ce: Muna zaune tare da shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ga mai kiwon tumakan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana korosu zuwa gurin kwanciyarsu, kuma yana ɗauke da jaririn ɗan bunsuru yana kuka, sai ya ce: Me aka haifa maka? Ya ce: Mace. Ya ce: To ka yanka mana wata akuyar babba a madadinta, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Kada ka yi zatan cewa mu saboda ku ne muka ɗorawa kanmu muka yanka muku ba, kawai mu muna da wasu tumakai ne guda ɗari, bama son adadin ya ƙaru akan wannan adadin, idan aka haifi sabon jinjiri sai mu yanka wani a madadinsa, Laƙiɗ ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, lallai cewa matata mai dogon harshe ce kuma mai alfasha ce, ya zan yi da ita? Ya ce: To ka saketa kawai. Ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah lallai tana tare da ni tuntuni, kuma akwai zuriya a tsakakninmu. Ya ce: To ka yi mata wa'azi, idan akwai alheri a tare da ita to zata ji wa'azinka, idan bata ji wa’azinba to ka daketa dukan da bazai sa rauni ba, kada ka daketa kamar yadda kake dukan bayinka. Sannan Laƙiɗ ya ce: Ya Manzon Allah, ka bani labari game da alwala. Ya ce: Ka isar da ruwa bigirensa a lokacin alwala, kuma ka cikawa kowace gaɓa haƙƙinta, kada ka bar wani abu daga cikin farillan alwala da sunnoninta, ka rarraba yatsun hannayenka da ƙafafuwanka a lokacin wanketa, kuma ka kai matuƙa a shaka ruwa a cikin hancinka a lokacin alwala da kuma fitar da shi saidai idan ka kasance ka ƙulla alwala dan kada ruwa ya shiga cikinka.